IQNA

22:22 - December 12, 2019
Lambar Labari: 3484312
An gudanar da taron tattaunawa tsakanin musulmi da kista a birnin Berlin na kasar Jamus.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a jiya aka gudanar da wani taron tattaunawa tsakanin musulmi da kista a birnin Berlin na kasar Jamus a karo na biyar.

Hojjatol Islam Nasir Niknejad shuggaban cibiyar muslunci ta Berlin, da kuma Hamid Muhammadi jakadan Iran na daga cikin wadanda suka halarci zaman taron.

Babban abin da aka tattauna a taron dais hi ne kara karfafa hanyoyin samun fahimta tsakanin mabiya addinin biyu, wato muslunci da kuam kiristanci.

Haka nan kuma an duba wasu daga cikin kalu bale da dukkanin bangarorin biyu suke fuskanta, tare da tattauna hanyoyin warware wadannan kalu bale ta hanyoyin da suka dace.

 

https://iqna.ir/fa/news/3863650

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Berlin ، Jamus ، wani taro
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: