IQNA

15:06 - December 26, 2019
Lambar Labari: 3484349
Ana gudanar da tarukan kirsimati a yankin zirin Gaza na Falastinu tare da halartar kiristoci da musulmi.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, tun a daren shekaran jiya aka fara gudanar da tarukan kirsimati a yankin zirin Gaza na Falastinu tare da halartar kiristoci da musulmi a dukkanin yankin baki daya.

Kamar dai yadda aka saba yi kowace shekara, a bana ma mabiya addinin irista tare da musulmia  dukkanin yanunan zirin gaza na palastinu suna gudanar da bukukuwan kirsimati tare.

Wannan yanayi ne da aka san al’ummar falastinu da shi tun tsawon tarihi, inda musulmi da kiristci suke rayuwa tare a cikin amince da yarda da juna, inda dukkanin bangarorin suke shiga cikin dukkanin lamarin da ya shafi daya bangaren, ko na murna ko ko bakin ciki.

A lokacin bukukuwan kirsimati, musulmi suna taya kiristoci murna, kuma suna halartar wuraren tarukansu, kamar yadda musulmi sukan saka abubuwa da nuna alamar bikin kirsimati, kamar itatuwa masu dauke ad fitilu.

Haka nan kuma mabiya addinin kirista suna halartar dukkanin tarukan musulmi a zirin Gaza na falastinu, kamar yadda suka halarci hatta wuraren buda baki na musulmi a lokacin azumi.

Hakan nan kuma a cikin watan Ramadan kiristoci basa cin abinci a bainar jama’a, yayin da wasu daga cikin kiristocin ma suna yin azumi domin girmama watan da musulmi suke yin azumi a cikinsa, da dai sauranabubuwa da ke nuni da kyakkawar alaka da girmama juna da ke tsakaninsu.

https://iqna.ir/fa/news/3866749

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: