IQNA

23:56 - March 21, 2020
Lambar Labari: 3484642
Tehran (IQNA) jagoran kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa Alfakhuri ya fice tare da taimakon Amurka.

Jagoran kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrallah wanda ya bayyana haka a wani jawabi da ya gabatar da jiya Juma’a da dare, ya kuma kara da cewa; Wajibi ne mu yi la’akari da cewa da akwai yakin da ake yi domin rusa gaskatawar da al’umma su ka yi wa gwagwarmaya wacce ta ke kalubalantar haramtaciyar kasar Isra’ila.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah wanda ya yi magana akan wani dan leken asirin Isra'ila A’mir al-Fakhuri wanda wata kotun kasar ta Lebanon ta wanke shi daga dukkanin laifukan da ya aikata, ya kara da cewa; Yin magana akan wannan batun ya zama wajibi domin warware wa magoya bayan gwgawarmaya hakikanin abinda ya faru, domin su ne ake son a yi wa yankan baya.

Sayyid Nasrallah ya kara da cewa; Tun farkon batun na al-Fakhuri, Amurka ta rika yin matsin lamba akan jami’a kasar Lebanon, wani lokacin da yin barazana kai tsaye ta kakaba takunkumi da dakatar da bai wa sojojin Lebanon tallafi da taimako.

Sayyid Nasrallah ya kara da cewa; Abinda ya faru yana cike da darussa domin wani yanki ne na yakin da yake gudana da yake ci gaba da abokan gaba.

 

3886688

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: