IQNA

22:46 - March 26, 2020
Lambar Labari: 3484659
Tehran (IQNA) kwamitin manyan malaman addini a cibiyar Azhar ta kasar ya fitar da fatawar da ta hana sallolin Jama’i da Juma’a.

Jaridar Tribune ta kasar Pakistan ta bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Pakistan Arif Alawi ne ya bukaci wannan fatawa daga cibiyar ta Azhar.

Ya zo a cikin wannan fatawa cewa, bisa la’akari da cewa taruwar mutane a wuri guda na iya jawo yaduwar cutar corona, saboda haka ya halasta a dakatar da sallolin jam’i da kuma sallolin Juma’a.

Fatawar ta ce ya zama wajibi a kan gwamnatocin kasashen musulmi da su dauki matakai, daga cikin har da hana sallolin jam’i, domin kaucewa yaduwar annobar a tsakanin al’umma.

Ya zuwa yanzu mutane kimanin dubu 450 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar corona a duniya, yayin da fiye da dubu 19 da 800 daga cikinsu suka rasa rayukansu.

 

3887434

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: fatawa ، cibiyar azhar ، Masar ، malaman addini ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: