IQNA

23:35 - April 02, 2020
Lambar Labari: 3484675
Tehran (IQNA)Babban kwamandan sojojin kasar Iran Janar Mohammad Bakiri ya bayyana cewa sojojin kasar suna kallon duk kai kawon Amurka a yankin gabas ta tsakiya.

A yau ne babban kwamandan sojojin kasar Iran Janar Mohammad Bakiri ya bayyana cewa sojojin kasar suna sanya idi da kyau a kan duk wani motsi na sojojin a yankin baki daya, sannan ya kara da cewa ba ruwan kasar Iran da hare-haren da ake kaiwa sojojin Amurka a kasar Iraqi a halin yanzu.

Babban kwamandan sojojin kasar na Iran ya kara da cewa Amurka ta san cewa mutanen kasar Iraqi ba sa son zamansu a kasar don kisan da ta yiwa Janar Sulaimani da kuma Abu Mahdi Al-Muhandis, don haka suna da hakkin maida martani kan sojojin kasar ta Amurka da suke mamaye da kasarsu.

Haka nan janar Bakiri ya ce sojojin kasar suna kula da kan iyakokin kasar ta sama da kasa don tabbatar da cewa ba wanda ya keta hurumin kasar.

Kamar yadda kuma ya karyata cewa sojojin kasar suna shirin kaiwa Amurka hare-hare a kasar Iraqi kamar yadda Amurkan ta bayyana a baya-bayan nan a ta akin jam’anta.

 

 

3888680

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: janar Baqiri ، Iran ، Amurka ، take-taken ، Abu Mahdi Al-Muhandis ، hare-hare
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: