IQNA

Azhar Ta Haramta Cin Zarafin Wadanda Suka Kamu Da Corona

23:45 - April 12, 2020
Lambar Labari: 3484704
Tehran (IQNA) cibiyar Azahar ta fitar da fatawar haramta cin zarafi ko keta alfarmar masu dauke da cutar corona.

Shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, cibiyar Azahar ta kasar Masar ta fitar da fatawar haramta cin zarafi ko keta alfarmar masu dauke da cutar corona a raye ko bayan mutuwarsu.

Haka nan kuma Azhar ta ce yin karya a kan wadanda cutar ta kama shi ma haram ne, musulmi ne ko ba musulmi, kuma wajibi ne a taimaka masa da dukabin da za a iya.

Wannan fatawa ta Azhar ta zo sakamakon matakin da mutanen wani gari a Masar suka dauka, na hana rufe gawar wata likita a makabartar garin, wadda ta rasu sakamakon kamuwa da corona, inda suke ganin rufe gawarta  a garin zai jawo yaduwar cutar corona a garin nasu.

 

3890968

 

Abubuwan Da Ya Shafa: haramta ، cibiyar azhar ، Masar ، musulmi ، yaduwar ، cutar corona ، likita
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha