IQNA

23:53 - June 11, 2020
Lambar Labari: 3484885
Tehran (IQNA) Paparoma Francis ya bayar da taimakon kudade ga mutanen da suka samu matsalaoli sakamakon bullar Corona.

Shafin yada labarai na Arab news ya bayar da rahoton cewa, a cikin Paparoma ya bayar da tallafin kudi da suka kai dalar Amurka miliyan 1.3 domin taimaka ma mutane masu karamin karfi da corona ta kassara su a birnin Rom na Italiya.

Cibiyar agaji ta caritas da ke karkashin fadar Vatican a birnin Rom na kasar Italiya ta bayyana cewa, wannan taimako shi ne karon farko wanda zai shafi mutanen da ba su da galihu, kuma ba su samu tallafi daga gwamnati ba a cikin irin wannan mawuyacin hali da aka shiga sakamakon bullar corona.

Pascole Marano, wani babban malimin kirista ne a yankin San Giovanni da ke cikin Rom ya bayyana cewa, akwai babban dakin dafa abinci mallakin fadar Katolika da ke yankin, wanda ke raba abinci ga dubban mutane mabukata a kowace rana.

Marano ya ce taimakon kudin da Paparoma ya bayar za a raba shi ne ga masu karbar abinci a wurin, kuma a cewarsa akasarin mutanen da suke zuwa wurin musulmi ne wadanda suka yi hijira zuwa kasar Italiya, saboda haka su ne za su fi samun kaso mafi yawa daga cikin wannan taimako.

 

 

3904154

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: paparoma francis ، taimako ، mafi yawa ، Italiya ، kaso mafi ، yawa ، gudun hijira
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: