IQNA

Kayayyakin Bukatar Rayuwar Al’umma Na Gab Da Karewa A Yemen

21:12 - June 17, 2020
Lambar Labari: 3484902
Tehran (IQNA) Hukumar agajin gaggawa ta majalisar dinkin duniya ta sanar da cewa, kayayyakin taimako da kungiyoyi na kasa da kasa  suke baiwa al’ummar kasar Yemen na gab da karewa.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, reshen hukumar bayar da agajin gaggawa ta majalisar dinkin duniya a kasar Yemen ya sanar da cewa, kayayyakin taimako da kungiyoyi na kasa da kasa suke baiwa al’ummar kasar ta Yemen na gab da karewa baki daya.

Rahoton hukumar ya ce, jama’a suna cikin mawuyacin hali, a daidai lokacin da saudiyya take ta kara tsananta hare-harenta  akan al’ummar kasar, inda hukumar ta ce tana bayanin cewa fararen hula 15 ne suka rasa rayukansua  hare-haren da saudiyya ta kaddamar a lardin sa’adah da ke arewacin Yemen a ranar Litinin da ta gabata, daga cikinsu har da kananan yara guda 4.

Hukumar agajin ta majalisar dinkin duniya ta ce akwai bukatar kai agajin gaggawa ga al’ummar kasar ta Yemen tun kafin lokaci ya kure, domin kuwa dukkanin kayayyakin bukatar rayuwa da al’ummar suke da su na gab da karewa.

Rahoton hukumar agajin ta majalisar dinkin duniya na zuwa ne kwana daya bayan fitar da rahoto da babban sakataren majalisar dinkin duniyar Antonio Guterres ya yi ne, inda a  ciki rahoton nasa ya cire saudiyya daga cikin kasashen da suke keta hakkokin kananan yara, bayan da kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suka mika bayanai da ke zarginta da hakan, musamman ma kan abin da take aikatawa a kasar  Yemen.

3905411

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :