IQNA

22:45 - September 22, 2020
Lambar Labari: 3485209
Tehran (IQNA) jagoran kungiyar Ansarullah (Alhuthy) ta Yemen ya bayyana kulla alaka da Isra’ila da wasu larabawa suke yi da cewa ya kara fito da masu munafuntar musulmi a fili.

Shugaban yunkurin “Ansarullah” na kasar Yemen, Abdulmalik al-Huthy ya bayyana cewa; Masu kulla alaka da Isra’ila suna amfani da karfi akan al’ummunsu, yayin da su ke kaskantar da kawukansu ga Amurka da Isra’ila.

Abdumalik Huthy wanda ya gabatar da jawabi dangane da juyin ranar 21 ga watan Satumba a kasar Yemen ya kara da cewa, a wannan lokacin ana bayyana wadanda su ke riko da hakkokinsu a matsayin masu kiyayya da zaman lafiya.

Har ila yau shugaban yunkurin na “Ansarullah” ya yi ishara da yadda Amurkawa su ka kafawa kasar Yemen kahon zuka da takura ma ta saboda kasantuwarta a bagire mai muhimmanci da kuma rawar da za ta iya takawa a tsakanin al’ummar musulmi.

Bugu da kari, Huthy ya ce; Abin da Amurkan take yi shi ne raba kasar ta Yemen da dukkanin karfin da take da shi, sannan kuma da haddasa rabuwar kawuna a tsakanin al’ummar kasar.

3924447

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: