IQNA

Macron Ya Sake Maimata Kalaman Batunci A Kan Addinin Muslunci

20:45 - October 30, 2020
Lambar Labari: 3485321
Tehran (IQNA) shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sake maimaita kalamansa na sukar addinin muslunci.

Duk da yin tir da Allawadai da daukacin kasashen musulmi suka yi da harin da wani ya kai a coci a garin Nice na kasar Faransa tare da kashe mutane uku, shugaban kasar Faransa ya sake maimaita kalamansa na sukar addinin muslunci.

Harin wanda aka kai a jiya a kan majami’ar mabiya a ddinin kirista a garin Nice na kasar Faransa, wanda wani musulmi ya kai, tare da kashe mutane uku dukkaninsu fararen hula, ya fuskanci kakkausar suka daga al’ummomin musulmi a  ko’in cikin fadin duniya.

Wannan ne yasa musulmin kasar Faransa suka janye gudanar da bukukuwan maulidin manzon Allah da suka shirya, domin yin alhinin abin da ya faru, tare da fitar da bayanai da ke yin tir da hakan, da kuma tabbatar da cewa duk wanda ya aikata baya wakiltarsu a matsayinsu na musulmin kasar Faransa.

Duk da irin wannan matsaya da musulmin kasar Faransa suka dauka da ma sauran musulmi na duniya da ke yin tir da abin da faru, da kuma nisanta haka da mahnaga ta addinin muslunci, amma shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron ya sake maimata kalamansa na sukar addinin musl;unci, tare da bayyana abin da ya faru da cewa ta’addanci ne na musulunci.

Kafin wannan lokaci dai al’ummomin musulmi sun nuna bacin ransu da kalaman da ya yi a cikin ‘yan kwanakin makamanta hakan, inda yake kokarin nuna cewa aikin ta’addanci yana damfare ne da akidar addinin muslunci.

3932059

 

captcha