IQNA

Jagoran Juyi Na Iran Da Sayyid Nasrullah Na Daga Cikin Musulmi Da Suka Fi Tasiri A Shekara ta 2020

17:26 - April 04, 2021
Lambar Labari: 3485781
Tehran (IQNA) jagoran juyin juya halin musulunci na Iran da kuma babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon na daga cikin musulmi mafi tasiri a 2020.

An bayyana sunayen mutane 500 musulmi da suka fi tasiri a cikin shekara ta 2020 da ta gabata, sakamakon irin matsayarsu a kan lamurra daban-daban, da kuma wadanda suka nuna jarunta a kasashen da ba su da rinjaye inda suke fuskantar wariya.

Wata cibiyar kididdiga da ke da mazauni a birnin Amman na kasar Jordan ce take daukar nauyin gudanar da wannan bincike tare da fitar da sakamako a kowace shekara.

Binciken ya nuna cewa, Sayyid Ali Khamenei jagoran juyin juya halin musulunci na Iran na daga cikin mutane musulmi masu babban tasiri a  yanking abas ta tsakiya da ma kan wasu lamurra na duniya.

Baya ga haka kuma an bayyana Sayyid Hassan Nasrullah babban sakataren kungiyar Hizbullah a matsayin daya daga cikin mutane masu babban tasiri a yankin, dangane da matsayarsa kan lamurra da suka shafi siyasar yankin.

Haka nan kuma an zabi wasu mata daga kasashen India da China, wadanda suka nuna turjiya dangane da wariyar da suke fuskanta a wadannan kasashe, inda Bilkis Dadi tsohuwa ‘yar shekaru 82 da haihuwa daga kasar India ta zama daga cikin sahun gaba.

Wannan mata dai ta kasance tana zama a wani tanti tana zaman dirshan domin nuna rashin amincewa da wariyar da gwamnatin India take nuna wa musulmi, inda daga bisani wasu daruruwan mata suka bi sahunta, a kan haka jaridar Times ta kasar Burtaniya ta sanya ta a cikin jerin sunayen mata 100 jarumai na shekara ta 2020 da ta gabata.

3962200

 

captcha