IQNA

Guterres Ya Bukaci Da A Kawo Karshen Artabu A Birnin Quds Tsakanin Yahudawa Da Falastinawa

14:59 - April 28, 2021
Lambar Labari: 3485857
Tehran (IQNA) Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a kawo karshen kai ruwa rana da ake yi tsakanin yahudawa da kuma Falastinawa a birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a wata zantawa da ya yi da manema labarai a babban zauren majalisar dinkin duniya, mai magana da yawun babban sakataren majalisar Farhan Haq ya bayyana cewa, Antonio Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin yahudawan Isra’ila da kuam Falastinawa da ke birnin Quds das u kai zuciya nesa.

Ya ce babban abin da majalisar dinkin duniya ke bukata a halin yanzu shi ne dakatar da duk wani tashin hankali da artabu tsakanin bangarorin biyu, sannan a koma ga bin hanyoyi na sulhu da za su taimaka wajen samun zaman lafiya mai dorewa.

Sai dai anata bangaren kungiyar Human Rights Watch wadda take da babban ofishinta a birnin New York na kasar Amurka, ta zargi jami’an tsaron Isra’ila da aikata laifuka na zalunci da cin zarafi da take hakkokin Falastinawa a birnin Quds.

Bayanin kungiyar ya ce, abin da Isra’ila take yi a kan Falastinawa, daidai yake da abin da gwamnatin wariyar launin fata ta aikata a kasar Afirka ta kudu, a kan bakaken fata ‘yan asalain kasar.

 

3967458

 

 

 

captcha