IQNA

Dubban Mutane Sun Halarci Bizne Gawawwakin Musulmin Da Aka Kashe A Kasar Canada

23:01 - June 13, 2021
Lambar Labari: 3486007
Tehran (IQNA) dubban mutane ne suka halarci jana'izar iyalan nan Musulmai hudu da aka kashe a kasar Canada..

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, A Canada daruruwan mutane ne suka halarci jana'izar iyalan nan Musulmai su guda hudu da wani mahari ya abkawa da mota a ranar Lahadin data gabata a birnin Landan na Canadar.

An lullube gawar mamatan da turar kasar ta Canada, kafin daga bisani a yi masu jana’iza.

Harin dai ya bakanta rayukan mutane da dama, kuma Firaiministan kasar ta Canada, Justin Trudeau, ya danganta harin da na ta'addanci.

Kafin hakan dama ‘yan Sanda kasar, sun alakanta harin da na kiyaya, wanda aka kai ma mutanen kawai don suna musulmai.

A gobe Litini, ne ake gurfanar da matashin da ya bige mamatan da mota, wanda ake tuhuma da laifuka hudu na kisa.

 

3977082

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tuhuma ، musulmi ، kasar Canada ، wani matashi ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :