IQNA

An Kashe Wani Babban Kusa Na Taliban A Harin Da Aka Kai Asibitin Kabul

21:50 - November 03, 2021
Lambar Labari: 3486509
Tehran (IQNA) an kashe wani babban jigo a kungiyar a harin da aka kaddamar kan wani asibitia jiya a birnin Kabul.

Jaridar Indian Times ta bayar da rahoton cewa, an kashe wani babban jigo a kungiyar a harin da aka kaddamar kan wani asibitia jiya a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afghanistan.

Rahotannin sun ce an kashe babban kwamandan Taliban a hari da aka kai a wani asibiti a birnin Kabul a jiya. Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto jami'an Taliban na cewa Hamdallah Mukhlis na cikin wadanda aka kashe. Mokhles dan kungiyar Haqqani ne kuma jami'in soji na musamman.
 
Yana daya daga cikin manyan kwamandojin Taliban da suka shiga fadar shugaban kasa bayan da kungiyar ta kwace birnin Kabul tare da sanar da faduwar gwamnatin da ta gabata.
 
Daga nan ne aka nada shi kwamandan sojojin Kabul daga ma'aikatar tsaro ta Taliban da shugabannin kungiyar.
 
Asibitin Sardar Mohammad Daud Khan, kusa da ma'aikatar lafiya ta Afganistan, shi ne asibitin soja mafi girma a Afghanistan mai gadaje 400.
 

4010230

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: taliban kasar Afghanistan birnin Kabul
captcha