IQNA

Gobe ​​da yamma ne za a duba jinjirin watan Ramadan a kasar Saudiyya

18:35 - March 09, 2024
Lambar Labari: 3490773
IQNA - Kotun kolin kasar Saudiyya ta bukaci daukacin ‘yan kasar da su gabatar da sakamakon dubar ga kotun gunduma mafi kusa a gobe Lahadi 10 ga watan Maris, domin ganin watan Ramadan, ko dai da ido ko kuma da kayan aikin falaki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-Sabq cewa, cibiyar nazarin falaki ta kasa da kasa ta kasar Saudiyya ta sanar da cewa, ba zai taba yiwuwa a ga jinjirin watan Ramadan a ranar Lahadi 10 ga watan Maris ba daga wani yanki na kasashen Larabawa da na musulmi, ko dai da ido ko kuma da na’urar hangen nesa. Sai dai kotun kolin Saudiyya ta bukaci jama’a su fara duba jinjirin watan Ramadan daga yammacin Lahadi.

A cikin bayaninta, wannan cibiya ta yi ishara da matakin da aka dauka na ganin watan Sha'aban, inda ta sanar da cewa: 11 ga watan Fabrairun da ya gabata ita ce ranar daya ga watan Sha'aban, kuma ana sa ran musulmi a dukkan sassan kasar. A ranar Lahadi 29 ga watan Sha'aban ne kasar Saudiyya za ta gudanar da dubar jinjirin watan mai alfarma wanda ya yi daidai da 10 ga Maris.

Kotun kolin kasar Saudiyya ta bukaci duk wanda ya yi nasarar ganin jinjirin watan Ramadan da ido ko kuma ta hanyar wasu na’urori na zamani da suka yi amfani da ilmin falaki da ya gaggauta sanar da kotun gunduma mafi kusa da su sannan ya rubuta shaidarsa, ko kuma ya kira cibiyar lura da jinjirin watan Ramadan mafi kusa ya kai rahoto ga hukuma.

Har ila yau, wannan cibiya ta bukaci mutanen da suke da ikon ganin jinjirin wata da su je hedkwatar kula da jinjirin watan da ke sassa daban-daban na kasar, da su gabatar da kansu tare da baiwa masana hadin kai.

 

4204270

 

captcha