Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya bayyana damuwarsa kan kyamar da yakin Gaza ke haifarwa a tsakanin al'ummomin da za su zo nan gaba, ya kuma yi kira da a tsagaita bude wuta, a sako mutanen da aka yi garkuwa da su a zirin Gaza da kuma taimakon Falasdinawa.
Duk wannan wahalhalu da tashin hankalin da yake haddasawa da kuma kiyayyar da take shukawa a cikin al'ummu masu zuwa ya kamata su gamsar da mu cewa kowane yaki yana sa duniya ta yi muni fiye da da, in ji Paparoma.
Paparoma ya furta wadannan kalamai ne a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 10 da fara shirin samar da zaman lafiya wanda firaministan gwamnatin Sahayoniya Shimon Peres da kuma Mahmud Abbas shugaban hukumar Falasdinu suka amince da shi.
A wani bangare na jawabin nasa, Paparoma ya ce: A kowace rana ina addu'a cewa a karshe wannan yaki ya kare. Ina tunanin duk wadanda ke shan wahala a Isra'ila da Falasdinu, Kirista, Yahudawa da Musulmai.
Ya kara da cewa: Ina ganin ya kamata a yanke shawara daga karkashin baraguzan Gaza na kashe makaman, don haka ne nake kira da a tsagaita wuta. Ina tunani game da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da wuri-wuri kuma ina tunanin al'ummar Palasdinu kuma ina son tallafa musu ta yadda za su sami taimakon jin kai da suke bukata.
Paparoma ya jaddada cewa, dukkanmu ana bukatar mu yi kokari da himma wajen ganin an samu dorewar zaman lafiya da kasar Falasdinu da Isra'ila za su yi rayuwa kafada da kafada da bangon gaba da kiyayya.
A karshen jawabin nasa, Paparoma Francis ya ce: Dole ne dukkan mu mu kula da Kudus ta yadda za ta iya shaida haduwar 'yan uwantaka tsakanin Kiristoci, Yahudawa da Musulmai.