IQNA

An Karrama daliban kur'ani na kasar Yemen domin tunawa da shahid Ismail Haniyya

15:22 - August 05, 2024
Lambar Labari: 3491641
IQNA - An gudanar da bikin karrama daliban kur'ani na kasar Yaman su 721 a daidai lokacin da ake tunawa da shahidan Hafiz na kur'ani kuma mujahidan Palastinu Ismail Haniyyah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Khalij cewa, an gudanar da bikin yaye karatun kur’ani mai tsarki na 721 Hafiz daga cibiyoyin haddar kur’ani da ilimin addini na kasar Yemen da tunawa da sunan shahidan kur’ani Ismail Haniyya.

Bayan shahadar Isma'il Haniyyah, masu gudanar da wannan biki sun yanke shawarar sanya wa wannan shahidi suna na wannan karatun.

An gudanar da taron tunawa da karrama wadannan mahardatan kur'ani a birnin Taiz tare da halartar dimbin jama'a da jami'ai da dama.

Nasr Abdul Ghani Motahar, daya daga cikin wadanda suka shirya wannan kwas, ya ba da shawarar a cikin jawabinsa cewa, wadanda suka kammala karatun sun yi wa kansu ado da ladubban kur’ani, kuma su zama abin koyi a kan gaskiya, takawa da kuma shugabanci.

Ya ci gaba da jaddada cewa: Su sanya ma'abota haddar Alkur'ani a Gaza misalinsu, domin sun mutu ne saboda al'ummar musulmi.

 

 

 

4230162

 

captcha