IQNA

19:07 - February 02, 2017
Lambar Labari: 3481193
Bangaren kasa da kasa, Wasu kungiyoyin mata musulmi sun gudanar da tarukan ranar hijabin muslunci ta duniya, domin kara nuna goyon bayansu ga sauransu 'yan uwansu mata da ake muzguna musu a wasu kasashen duniya saboda saka hijabin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, Jaridar Guardian ta Najeriya ta bayar da rahoton cewa, kungiyoyin mata da dama ne suka gudanar da irin wadannan taruka, da suka hada har da kungiyar Muminat da kuma Standard.

Wadanann taruka da suka hada mata malaman jami'a da kuma daliban jami'oi musamman a biranan Lagos da kuma Ibadan, sun mayar da hankali ne wajen halin da sauran 'yan uwansu mata suke ciki a wasu kasashe da ake takura msuu saboda saka hijabi, musamamn a nahiyar turai.

Jahiya Mutiyat Orulo Balugon daya daga cikin wadanda shirya gudanar da wannan taro a Lagos ta bayyana cewa, babbar manufar taron ita ce karfafa mata musulmi kan mayar da hankali ga batun hijabin muslunci, domin kuwa hijabi ko ba komai umarni ne na Allah cewa mata su rufe jikinsu, baya hakan kuma akwai hikimomi da dama da suke kunshi a cikin wannan umarni na Allah.

Ta kara da cewa har yanzu ana take hakkokin mata musulmi a wasu sassa na Najeriya, inda ake takura musu a wasu makarntu ko wuraren aiki da sunan batun matsalar tsaro, alhali kuwa hana mata saka hijabi ba shi maganin matsalar tsaro da Najeriya ke fama da ita ba.

3569776


Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Najeriya ، Lagos ، Ibadan ، mata musulmi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: