Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Majiyoyin kungiyar red cross sun sanar da cewa, an shigar da manyan motoci kimanin arbain da shida dauke da kayan agaji, da suka hada da abinci, magunguna da dai sauransu, kuma za a raba kayan ne ga mutane dubu ashirin da bakwai da dari biyar.
Kafin wannan lokacin dai 'yan ta'addan sun hana mutane ficewa daga yankin, tare da yin barazanar kashe duk wanda ya yi yunkurin ficewa, bayan da gwamnatocin Syria da Rasha suka aike da manyan motocin bas-bas domin fitar da fararen hula daga yankin wanda 'yan ta'adda ke iko da shi.
'yan ta'addan da suka fito daga kasashen duniya daban-daban, suna yin garkuwa da dubban daruruwan fararen hula mazauna yankin, domin kare kansu daga farmakin dakarun Syria.