IQNA

Jiragen Saudiyya Sun Kai Hari Sau 300 A Yemen

23:59 - April 08, 2020
Lambar Labari: 3484693
Tehran (IQNA) Majiyar sojojin kasar Yemen ta bayyana cewa a cikin kwanaki bakawai da suka gabata, sojojin Saudiyya sun kai hare-hare kimanin 300 kan yankuna a kasar Yemen.

Kakkain sojan kasar ta Yemen birgediya Janar Yahya Sari’i  ya fadawa tashar talabjin ta al-masiriyya cewa sojojin kawancen Saudiyya sun kai hare-haren ne a lardunan San’aa, Bayda da kuma Ma’arib, inda suka kashe fararen hula da dama.

Yahyah Sari’i ya kammala da cewa sojojin kasar suna shirin maida martani nan ba da dadewa ba. Ya kuma kara da cewa dole ne mu kare mutanemmu mu kuma kare kasarmu daga makiya.

Tun cikin watan Maris na shekara dubu biyu da sha biyar ne gwamnatin kasar Saudiyya tare da takwarorinta na kasashen Larabawa kimanin goma suka farwa kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasar Abbdu Rabbu Hadi Mansur kan kujerar sugabancin kasar.

Yakin dai ya yi sanadiyar jefa mutane kimani miliyan ashirin da hudu cikin yunwa a kasar inji rahoton majalisar dinkin duniya, Sannan wasu miliyoyi kuma suka zama yan gudun hijira.

 

3890241

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen saudiyya hare-hare kan kasar kimanin
captcha