IQNA

Wani Malamin Kirista A Najeriya Ya Gina Wa Musulmi Masallaci A Wani Kauye Kusa Da Abuja

22:14 - August 27, 2021
Lambar Labari: 3486246
Tehran (IQNA) wani malamin addinin kirista a Najeriya ya gina wa musulmi masallaci a wani kauye da ke kusa da birnin Abuja.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a wata alama mai kyau ta karfafa zaman lafiya  tsakanin mabiya addinan kirista da musulmi a Najeriya, wani malamin addinin kirista mai suna Rev. Cleistos Isara, ya gina wa musulmi masallaci a wani kauye da ke kusa da birnin Abuja fadar mulkin kasar.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Anatli, Rev. Cleistos Isara ya bayyana cewa, tun a shekara ta 1998 ne suka je wannan kauyen domin yin wa'azin addinin kirista, duk kuwa da cewa akasarin mutanen kauyen mabiya addinin musulunci ne, amma ba su nuna kin amincewa da mu ba.

Ya ce maimakon haka ma sun samu tarba da grimamawa daga mai garin da kuma sauran mutane, wannan lamari ya faranta musu rai matuka, domin abin da ke da muhimamnci dama shi ne samun fahimtar juna da kuma zaman lafiya da girmama addini da akidar juna.

Ya ara da cewa, sun yi la'akari da cewa kauyen na fama da matsala a bangaren ilimi, saboda haka suka gina musu makarantu guda biyu na firamare da kuma makarantar share fagen shiga firamare.

Bayan nan kuma ya ce sun lura da cewa ginin masallacin garin ya lalce, saboda haka mutane suna yin salla ne a fili, wannan yasa ya kudiri aniyar sake gima ma musulmi wani masallacia  garin domin su samu wurin salla.

ساخت مسجد به دست کشیش کاتولیک در پایتخت نیجریه

Ya kara da cewa, a lokacin da ya kudiri aniyar yin haka, wasu daga cikin kiristoci sun nuna rashin amincewa, musulmi da kirista ba makiyan juna ba ne, kuma yin hakan abu ne mai kyau, domin kuwa zai kara karfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabya addinin biyu, da haka kuma ya gamsar da su.

An kuma bude masallacin ne tun a watan Mayu da ya gabata, kuma yanzu musulmi suna yin salloli biyar a cikin masallaci a kowace rana.

 

3993313

 

 

 

 

 

 

captcha