IQNA

23:26 - January 19, 2022
Lambar Labari: 3486843
Tehran (IQNA) ‘Yan Sanda Isra’ila sun ruguza gidan wasu iyalan Falasdinawa a unguwar Sheikh Jarrah dake gabashin birnin Qods.

‘Yan Sanda Isra’ila sun ruguza gidan wasu iyalan Falasdinawa a unguwar Sheikh Jarrah dake gabashin birnin Qods.

Bayanai sun ce bayan yunkurin yin hakan a lokuta da dama daga karshe ‘yan sanda na Isra’ila sun ruguza gidan da sanyin safiyar wannan Laraba.

Tun a shekarar 2017 ne ‘yan sanda na Isra’ila ke barazanar rusa gidan iyalan na Salhiya da ake kokarin kora daga yankin.

Gidan iayalan dai ya jima da yake samun goyan bayan al’ummar falasdinu har ma da na wasu kasashen ketare.

 

4029736

 

Abubuwan Da Ya Shafa: daga karshe ، barazana ، unguwar Sheikh Jarrah ، ‘yan sanda ، ruguza
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: