IQNA

23:44 - February 08, 2017
Lambar Labari: 3481213
Bangaren kasa da kasa, wata kotu a Amurka ta yanke hukuncin daurin shekaru 30 a gidan kaso a kan wani da yakona masallaci a garin Orlando na jahar Florida.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na STLToday cewa, joseph Schreiber dan shekaru 32 ya fuskanci hukuncin daurin shekaru 30 a gidan kaso, bayan samunsa laifin kona masallaci mallakin musulmi.

Mai laifin ya amsa cewa shi ne ya kone msallacin, ya ce ya yi hakan ne a a lokacin tunawa da cika shekaru sha biyar da kai harin 11 ga watan Satumba, domin kada jahar Florida ta zama wuri nag aba da musulmi za su kai harin ta’addanci.

Ya ce ya yi imanin cewa muslunci addinin ta’addanci ne, saboda hakan duk inda musulmi yake dan ta’adda ne, kuma jahar Florida tana ta kara karbar baki musulmi da suke zuwa, wanda hakan a cewarsa babbar barazana ce ga kasarsu.

joseph Schreiber bayahude ne dan kasar Amurka, wanda an sha samunsa da laifuka daban-daban, a kan haka kotu ta dauki matakin ladabtar da shi sakamakon kai ma masallacin musulmi hari tare da kone shi kurmus.

Muhammad malik daya daga cikin ‘yan kwamiti masu kula da masallacin ya bayyana cewa, masallacin ya lalace matuka a kan hakan sun canja wani wuri na daban domin gudanar da salla da kuma sauran ayyukan ibada.

3571614

Abubuwan Da Ya Shafa: IQNA ، Florida ، Amurka ، masallaci ، ibada ، musulmi ، kwamiti ، watan Satumba ، joseph Schreiber
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: