IQNA

Kungiyar Al-Azhar don yaki da tsattsauran ra'ayi:

Rage zaman dar-dar a Indiya ya dogara ne kan magance kalaman kyama ga musulmi

17:09 - August 01, 2022
Lambar Labari: 3487621
Kungiyar Al-Azhar da ke sa ido kan yaki da tsattsauran ra'ayi, yayin da take maraba da sakin 'yar jaridar Musulman Indiya, ta bayyana raguwar rikice-rikicen addini a Indiya da ya dogara da yaki da kyamar musulmi.

Kungiyar ta Al-Azhar, domin yaki da tsattsauran ra'ayi, yayin da take maraba da sakin 'yar jaridar Musulman Indiya da ta fallasa yadda jam'iyya mai mulki ke cin mutuncin addinin Musulunci, ta bayyana cewa ya zama wajibi a yaki da kyamar musulmi domin shawo kan rikicin addini a cikin al'ummar Indiya. A cewar wannan mai lura da al'amura, hakan zai zama wani share fage ga kwanciyar hankali da ci gaban Indiya.

Kafofin yada labaran Indiya sun rawaito cewa kotun kolin kasar ta bayar da umarnin a saki dan jarida dan kasar Indiya, Muhammad Zubair tare da dage haramcin buga ko yada a shafukansa na sada zumunta.

'Yan sandan Indiya sun kama Zubair bayan ya bayyana kalaman batanci da kakakin BJP ya yi wa Musulunci. A wancan lokacin wannan mai fallasa ya haifar da gagarumar zanga-zanga daga kasashen musulmi da dama na nuna adawa da Indiya.

Daga nan ne ‘yan sandan Indiya suka shigar da kara inda suka yi ikirarin cewa Mohammad Zubair ya ci mutuncin mabiya addinin Hindu ta hanyar wallafa wani sakon Twitter a shekarar 2018 tare da kama shi da laifin yada kiyayyar addini.

A wancan lokacin wani dan majalisar wakilai ya bayyana kama wannan dan jarida musulmi a matsayin wani hari da aka kai kan gaskiya tare da neman a sake shi, musamman da yake bai aikata wani laifi ba kamar yadda dokokin Indiya suka tanada.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4074913

Abubuwan Da Ya Shafa: tanada laifi musulmi wakilai maraba gaskiya
captcha