Bangaren kasa da kasa, A martanin da kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya mayar wa yarima mai j iran gado na masarautar Al Saud, ya bayyana cewa yana da kyau Bin Salman ya dauki darasi daga 'yan kama karya da suka gabace shi.
Lambar Labari: 3482136 Ranar Watsawa : 2017/11/25
Bangaren kasa da kasa, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa a duk inda aka bukaci taimako dmin fuskantar bakaken manufofin Amurka da makiya musulmi da musulunci toa shirye suke su kara.
Lambar Labari: 3482129 Ranar Watsawa : 2017/11/23
Bnagaren kasa da kasa, an gudanar da zaman taro karo na biyu kan masana na kasashen Iran da Senegal wato Allamah Tabataba'i da sheikh Malik Se.
Lambar Labari: 3482119 Ranar Watsawa : 2017/11/20
Bangaren siyasa, A yau da hantsi ne shugaba Rauhani na Iran ya isa yankin da girgizar kasa ta shafa a cikin Lardin kermanshah da ke yammacin kasar Iran, domin duba halin da al'ummar yankin suke ciki, musaman ma wadanda abin ya shafa.
Lambar Labari: 3482098 Ranar Watsawa : 2017/11/14
Bangaren kasa da kasa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana tuhumce-tuhumcen gwamnatin Saudiyya a kan Iran da cewa ba su da tushe balantana makama.
Lambar Labari: 3482071 Ranar Watsawa : 2017/11/06
Bangaren kasa da kasa, an zabi kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna a matsayin kafar yada labaran addini a mataki na farko a shekaru hudu a jere.
Lambar Labari: 3482061 Ranar Watsawa : 2017/11/03
Ayatollah Imami Kashani A Hudubar Juma’a:
Bangaren kasa da kasa, wanda ya jagoranci sallar Juma’a a Tehran ya bayyana cewa, babbar manufar makiya ta nuna raunana juyin muslunci a Iran ita ce kokarin ganin sun raunana dakarun kare juyin. Haka na kuma ya yi ishara da cewa batun karfin Iran babu batun tattaunawa akansa.
Lambar Labari: 3482044 Ranar Watsawa : 2017/10/27
Jagora:
Bangaren kasa da kasa, jagoran juyin juya halin muslunci ya bayyana yunkurin da wasu bangarori ke yin a neman saka makaman Iran a cikin abin da za a tattauana kansu da cewa lamari ne da ba zai yiwu ba.
Lambar Labari: 3482038 Ranar Watsawa : 2017/10/26
Bangaren kasa da kasa, cibiyar kula da al’adun muslunci ta kasar Iran ta shirya wa jami’oi biyar da ke kasar Pakistan gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki.
Lambar Labari: 3482014 Ranar Watsawa : 2017/10/19
Bangaren siyasa, Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Muhammad Ali Ja'afari ya bayyana cewa dakarunsa za su dauki sojojin Amurka tamkar 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh matukar dai Amurka ta sanya takunkumi da bata sunan dakarun nasa.
Lambar Labari: 3481981 Ranar Watsawa : 2017/10/08
Bangaren kasa da kasa, Jim Drami da Sulaiman Gey wasu masana biyu daga kasar Senegal sn ziyarci babban ofishin kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna.
Lambar Labari: 3481978 Ranar Watsawa : 2017/10/08
Shugaban Kasa:
Bangaren siyasa, shugaba Rauhani a okacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron makon kare kai ya bayyana cewa, Iran za ta ci gaba da kara inganta makamanta.
Lambar Labari: 3481921 Ranar Watsawa : 2017/09/22
Shugaba Raihani A Taron UN:
Bangaren siyasa, Shugaban Hassan Ruhani na kasar Iran ya bayyana jawabin da shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi a babban zauren majalisar dinkin duniya a jiya Talata da cewa, jawabin na trump ya kaskantar da kasar Amurka ne a gaban kasashen duniya.
Lambar Labari: 3481917 Ranar Watsawa : 2017/09/21
Jagoran Juyin Juya Hali:
Bangaren kasa da kasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ja kunne da cewa Iran za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliya da ta cimma da manyan kasashe to sai dai za ta mayar da martani ga duk wani karen tsaye ga yarjejeniyar.
Lambar Labari: 3481904 Ranar Watsawa : 2017/09/17
Bangaren kasa da kasa, an raba kayan agai da Iran ta aike zuwa kasar Bangaladesh domin raba su ga ‘yan gudun hijira na Rohingya da ke zaune a kasar.
Lambar Labari: 3481901 Ranar Watsawa : 2017/09/16
Bangaren kasa da kasa, Shugaba Rauhani na kasar Iran ya aike da sakonnin zuwa ga shugabannin kasashen musulmi, inda yake taya su murnar sallah, da kuma yi musu fatan alkhairi tare da al'ummomin kasashensu.
Lambar Labari: 3481853 Ranar Watsawa : 2017/09/01
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taron bayar da horo kan samun masaniya dangane da addinin muslunci wanda cibiyar muslunci ta Qom ta shirya a birnin Harare na Zimbabwe.
Lambar Labari: 3481812 Ranar Watsawa : 2017/08/19
Bangaren kasa da kasa, malama Cilindio Jengovanise daya ce daga cikin malaman da suke koyar da addinai musamman muslunci a jami’ar Zimbabwe.
Lambar Labari: 3481802 Ranar Watsawa : 2017/08/16
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba kuma ba za ta taba mika kai ga mulkin kama-karya na ma'abota girman kai, yana mai cewa a halin yanzu Iran tana tsaya da kafafunta kyam sama da shekarun baya.
Lambar Labari: 3481762 Ranar Watsawa : 2017/08/03
Bangaren kasa da kasa, Sayyid Ali Asgar Musawiyan matashi dan kasar Iran mai fasahar rubutu ya bayar da kyautar kwafin kur'ani ga hubbaren Abbas (AS).
Lambar Labari: 3481753 Ranar Watsawa : 2017/07/31