IQNA

Matsayar Musulunci Dangane Da Corona A Mahangar Mujallar Amurka

23:15 - March 22, 2020
Lambar Labari: 3484646
Tehran (IQNA) mujallar News Week ta kasar Amurka ta kawo bayani kan mahangar annabin musulunci (SAW) kan wajabcin tsafta da kuma wajacin kare kai daga kamuwa da cututtuka.

Shahararren marubuci kuma malamin jami’a masani kan ilimin zamantakewar al’ummomi CRAIG CONSIDINE, wanda ya rubuta wata makala wadda mujallar ta buga, a ciki yana fadin cewa, cutar covid-19 cuta wadda ta mamaye duniya a halin yanzu kuma ake neman mafita dangane da ita ido rufe.

Ya ce wane mutum ne wanda ya fara bayar da mafita domin kaucewa kamuwa da cututtuka, da kuma yadda za a kaucewa yaduwarsu? Sai ya bayar da masa da cewa; annabin muslunci kimanin shekaru 1400 ya bayar da mafita kan yadda za a tunkara matsaloli irin s corona.

Ya ce annabin musulunci ya ce idan kuka labarin wata annoba ta bulla a wata kasa, to kada ku je can, idan kuma a nda kuke ta bulla to kada ku fita zuwa wasu wurare, idan kuma kuma kamu da cuta, kada ku shiga cikin sauran mutane domin kada ku yada mus ita.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, addinin muslunci ya wajabta tsafta a kan mabiyansa, har ma ya sanya tsafta ta zama daga cikin imani, kamar yadda kuma idan rashin lafiya ta kama wani ya kan bayar da shawarar yin magani.

Ya ce akwai hikima da yin amfani da hankalia  cikin dukkanin matakan da Muhammad yake dauka, wadanda kuma suna a matsayin mafita ga al’ummarsa tun a wancan lokaci, a yanzu ma yin aiki da wannan mahanga tasa tana matsayin mafita wajen hana yaduwar corona.

3886901

 

captcha