iqna

IQNA

Bangaren kasa da kasa, an karama mahardata kur’ani 350 da suka nuna kwazo a gasar kur’ani ta watan Ramadan a lardin Manufiyyah na kasar Masar.
Lambar Labari: 3482763    Ranar Watsawa : 2018/06/16

Bangaren kasa da kasa, dan kasar Iran ne ya lashe gasar mafaza ta tashar alkawsar ta talabijin da maki 84.
Lambar Labari: 3482762    Ranar Watsawa : 2018/06/15

Bangaren syasa, al'ummar Iran kamar sauran mafi yawan al'ummun duniya a yau Juma'a ne suka gudanar da sallar idi karama wata idir fitir karkashin limancin Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran a hubbaren Marigayi Imam Khomeini da ke birnin Tehran.
Lambar Labari: 3482761    Ranar Watsawa : 2018/06/15

Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar: Matsalar haramtacciyar kasar Isra'ila ita ce rashin halalci, don haka da yardar Allah da kuma himmar al'ummar Musulmi, ko shakka babu za a kawar da ita da kuma kawo karshenta.
Lambar Labari: 3482760    Ranar Watsawa : 2018/06/15

Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta yi gargadi dangane da halin da za a jefa al’ummar Yemen sakamakon hare-haren mayakan Hadi a gabar ruwan Hodaidah ta Yemen.
Lambar Labari: 3482759    Ranar Watsawa : 2018/06/14

Bangaren kasa da kasa, Wasu mahara sun kai farmaki cikin wani Masallaci a shiyar kudu maso yammacin kasar Afrika ta Kudu, inda suka kashe mutane biyu.
Lambar Labari: 3482758    Ranar Watsawa : 2018/06/14

Bangaren kasa da kasa, Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tana ci gaba da tattaunawa domin kaucewa zubar da jini a birnin Hodeida na kasar Yemen, inda kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kaddamar da hari a yau Laraba.
Lambar Labari: 3482757    Ranar Watsawa : 2018/06/14

Bangaren kasa da kasa, shugaba Rauhani na Iran ya aike da sakonnin taya murnar kammala azumin watan ramadan zuwa ga shugabannin kasashen musulmi.
Lambar Labari: 3482756    Ranar Watsawa : 2018/06/14

Bangaren kasa da kasa, babban mai shiga tsakani na gwamnatin Palastinu Saib Uraqat ya bukaci kungiyar tarayyar turai da amince da kasar Palastinu mai ci gishin kanta.
Lambar Labari: 3482755    Ranar Watsawa : 2018/06/13

Bangaren kasa da kasa, an kame wani mutum dan shekaru 35 da yake aikewa da wasiku yana yi musulmi barazana a kasar Birtaniya.
Lambar Labari: 3482754    Ranar Watsawa : 2018/06/13

Bangaren kasa da kasa, ofishin babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya bada umarnin duba watan shawwal gobe alhamis a fadin kasar.
Lambar Labari: 3482753    Ranar Watsawa : 2018/06/13

Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen gasar kur’ani ta Mustaqbal watan a garin Ukdah da ke cikin gundumar sharqiyyah a Masar.
Lambar Labari: 3482752    Ranar Watsawa : 2018/06/12

Bangaren kasa da kasa, an sanar da sunayen wadanda suka lashe gasar kur’ani mai tsarki ta kasar Aljeriya.
Lambar Labari: 3482751    Ranar Watsawa : 2018/06/12

Bangaren kasa da kasa, fiye da mutane miliyan biyu nesuka halaci sallar daren 27 ga watan Ramadan da zimmar riskar daren lailatul qadr a Ka’abah.
Lambar Labari: 3482750    Ranar Watsawa : 2018/06/12

Bangaren kasa da kasa, a daren yau ne za a rufe gasar kur’ani ta duniya karo na goma sha biyar a kasar Aljeriya.
Lambar Labari: 3482749    Ranar Watsawa : 2018/06/11

Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta daliban makarantun firamare da sakandare a kasar Ghana.
Lambar Labari: 3482748    Ranar Watsawa : 2018/06/11

Bangaren kasa da kasa, a yau ne za a bude babbar gasar kur’ani ta kasa da kasa a binin Nuwakshout na kasar Mauritania.
Lambar Labari: 3482747    Ranar Watsawa : 2018/06/11

Bangaren kasa da kasa, cibiyar Muhammad Bin Rashid a hadaddiyar daular larabawa tare da cibiyar buga kur’anai ta Saudiyya za su buga tafsiran kur’ani.
Lambar Labari: 3482746    Ranar Watsawa : 2018/06/10

Bangaren kasa da kasa, kasar Iran ta dauki nauyin shiryawa musulmin kasar Rasha wani buda baki a birnin Moscow fadar mulkin kasar.
Lambar Labari: 3482745    Ranar Watsawa : 2018/06/10

Bangaren kasa da kasa, gungun makaranta kur’ani na Taha sun isa kasar Afirka ta kudu inda suka gudanar da karatu a Pretoria.
Lambar Labari: 3482744    Ranar Watsawa : 2018/06/10