کد خبر: 1281565
تاریخ انتشار : ۱۰ شهريور ۱۳۹۲ - ۱۷:۵۸

Kai hari kan al’ummar kasar Syria kamar hari ne kan al’mmomin musli da na larabawa

Bangaren kasa da kasa, Wanda ya jagoranci sallar Juma'ar birnin Tehran a yau ya bayyana cewar babu wani abin da Amurka da kawayenta za su samu cikin hari ga kasar Siriya in ban da hasara da kuma kara kyamar da al'ummar musulmi da sauran al'ummomi suke musu.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da hudubar sallar Juma'a a masallacin Juma'a na birnin Tehran, babban birnin Jamhuriyar Musulunci ta Iran inda ya ce ko shakka babu al'ummar Siriya za su yi nasara kan wannan makirci da ake kulla musu sakamakon irin tsayin daka da gwagwarmayar da aka sansu da shi.


Sheikh Siddiqi ya kara da cewa ba abin da wannan hari da Amurka take shirin kai wa kasar Siriya in ban da dagula lamurran tsaro da zaman lafiya a duniya, don haka ya ja kunnen Amurkawan da kawayensu da su guji hakan.


Yayin da ya koma kana bin da ke faruwa a kasar Masar kuwa, na'ibin limamin na Tehran ya kirayi al'ummar kasar da su hada kansu waje guda don nesantar yakin basasa da ake kokarin tayarwa a kasar.


Jakadan kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ce take karfafa gwiwar kasar Amurka kan kaddamar da hare-haren soji kan kasar Siriya.


A jawabin da ya gabatar bayan kammala zaman kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin kasar Siriya; Jakadan Siriya a Majalisar Dinkin Duniya Bashar Ja'afari ya jaddada cewar gwamnatin Siriya ba ta yi amfani a wani makami mai guba wajen kai hari a cikin kasarta ba, kuma tun bayan bullar labarin amfani da makami mai guba a kasar ta Siriya, gwamnatin Bashar Asad ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta hanzarta gudanar da bincike kan lamarin.


Har ila yau Ja'afari ya fayyace cewar kasashen Saudiyya, Qatar da Turkiyya ne suke tallafawa 'yan ta'addan kasa da kasa da aka jibge a cikin kasar Siriya da makamai tare da karfafa musu gwiwar yin amfani da makamai masu guba da nufin juya akalar laifin kan gwamnatin Siriya, sannan ita kuma gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta ingiza gwamnatin Amurka kan yin amfani da karfi kan kasar Siriya.


A karshe dai jakadan kasar ta Siriya ya yi gargadi kan mummunan sakamakon da hare-haren wuce gona da iri kan kasar ta Siriya zai haifar a dukkanin yankin gabas ta tsakiya.



1281497





captcha