Bangaren kasa da kasa, Maimuna Lu wata mahardaiyar kur’ani mai tsarki daga kasar Senegal za ta halarci gasar kur’ani ta Auqaf da za a gudanar a Iran.
Lambar Labari: 3482573 Ranar Watsawa : 2018/04/15
Bangaren kasa da kasa, an nuna makalar wani masani dan kasar Iran a matsayin daya daga cikin fitattun makaloli a taron kasa da kasa kan ilmomin kur’ani.
Lambar Labari: 3482572 Ranar Watsawa : 2018/04/15
Sayyid Hassan Nasrullah:
Bangaren kasa da kasa, jagoran kungiyar Hizbullah ya bayyana cewa, takaita hare-haren da Amurka ta jagoranta kan Syria ya tabbatar da karfin sojin Syria da gungun masu gwagwarmaya.
Lambar Labari: 3482571 Ranar Watsawa : 2018/04/15
Bangaren kasa da kasa, an karrama yara 20 mahardata kur'ani a lardin Qana na Masar.
Lambar Labari: 3482570 Ranar Watsawa : 2018/04/14
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin Siriya ta danganta hare haren sojin da kasashen Amurka, Birtaniya da Faransa suka kai mata a cikin daren jiya da keta dokokin kasa da kasa da hurimin da kasar take da shi.
Lambar Labari: 3482569 Ranar Watsawa : 2018/04/14
Bangaren kasa da kasa, Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar da zaman gaggawa a yau, domin tattauna harin da kasashen Amurka da Birtaniya gami da Faransa suka kaddamar a kan Syria.
Lambar Labari: 3482568 Ranar Watsawa : 2018/04/14
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya bayyana harin da Amurka da Birtaniya gami da Faransa suka kaddamar kan Syria a da jijjifin safiyar yau a matsayin babban laifi, kuma ma'abota girman kai tabbas daga karshe za su sha kayi.
Lambar Labari: 3482567 Ranar Watsawa : 2018/04/14
Bangaren kasa da kasa, shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela markel ta bayyana cewa, kasarta ba za ta shiga cikin duk wani shirin kaddamar da harin soji a kan kasar Syria ba.
Lambar Labari: 3482566 Ranar Watsawa : 2018/04/13
Bangaren kasa da kasa, dakarun Yemen tare da mayakan Ansarullah sun harba makamai masu linzami kan yankin tsaro na Al-faisal da ke gundumar Jazan a Saudiyya.
Lambar Labari: 3482565 Ranar Watsawa : 2018/04/13
Bangaren kasa da kasa, tawagar masu gudanar da bincike na hukumar hana yaduwar makamai masu guba sun isa Syria domin gudanar da bincike.
Lambar Labari: 3482564 Ranar Watsawa : 2018/04/13
Bangaren kasa da kasa, soojojin yahudawan Isra’ila sun harbe wani bafalastine har lahira a kusa da iyakokin Gaza da yankunan palastinawa da Isra’ila ta mamaye, a ci gaba da murkushe yunkurin falastinawa na nuna rashin amincewa da mamaye musu kasa.
Lambar Labari: 3482563 Ranar Watsawa : 2018/04/13
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya wadda ta kebanci daliban jami'a a yankin karabuk na kasar Turkiya.
Lambar Labari: 3482562 Ranar Watsawa : 2018/04/12
Bangaren kasa da kasa, dakarun saman kasar yemen sun kai hari da makamai masu Linzami a filin sauka da tashi na jiragen Abha na da kuma cibiyar Man fetir na Aramko dake kasar Saudiya.
Lambar Labari: 3482561 Ranar Watsawa : 2018/04/11
Bangaren kasa da kasa, a yau Jiragen yaki na kawancan da Amurka take jagoranta sun yi shawagi a kan iyakar Iraki da Syria.
Lambar Labari: 3482560 Ranar Watsawa : 2018/04/11
Bangaren kasa da kasa, Muhaammad Mahdi Haqgoyan makarancin kur’ani mai tsarki yi karatun kur’ani mai tsarki a cibiyar Imam Ali (AS) da kasar Sweden.
Lambar Labari: 3482559 Ranar Watsawa : 2018/04/11
Bangaren kasa da kasa, Babbar mai shigar da kara a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya Fatou Bensouda, ta bukaci a gudanar da bincike kan kisan kiyashin da aka yi wa 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.
Lambar Labari: 3482558 Ranar Watsawa : 2018/04/10
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Ibrahimi wata cibiya ce da take bayar da gudunmawa wajen horar da yara kan tarbiya ta kur'ani wadda aka samar tun 2009.
Lambar Labari: 3482557 Ranar Watsawa : 2018/04/10
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani shiri nahorar da ladanai masu kiran salla a kasar Tunisia.
Lambar Labari: 3482556 Ranar Watsawa : 2018/04/10
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra’ila na shirin mayar da masallacin tarihi na Zahir Uma Zaidani da ke garin Tabriyya na Palastinu zuwa wani wurin kasuwanci.
Lambar Labari: 3482555 Ranar Watsawa : 2018/04/09
Bangaren kasa da kasa, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun harbe Sheikh Salama kasiri wani babban malmin addini a garin Siun na Hadra Maut a Yemen.
Lambar Labari: 3482554 Ranar Watsawa : 2018/04/09