کد خبر: 1278537
تاریخ انتشار : ۰۴ شهريور ۱۳۹۲ - ۱۷:۵۸

An dage shari'ar tsohon shugaban kasar Masar da 'yan uwa musulmi

Kasa da kasa, kotun da take sake gudanar da shari'ar tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ta dage zaman shari'ar zuwa ranar 14 ga watan Satumban wannan shekara da muke ciki.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Majiyar shari'ar kasar Masar ta bayyana cewar tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak ya gurfana a gaban kotu a jiya Lahadi bayan sakinsa daga gidan kurkuku a ranar Alhamis da ta gabata, inda a halin yanzu yake fuskantar shari'a kan zargin hannu a kashe masu gudanar da zanga-zangar lumana a lokacin boren neman kawo karshen gwamnatinsa ta kama karya a shekara ta 2011.


Majiyar ta kara da cewar daga cikin mutanen da suka gurfana a gaban kotun a jiya Lahadi sun hada da 'ya'yayen tsohon shugaban kasar guda biyu da kuma tsohon ministan harkokin cikin gidan Masar gami da wasu manyan jami'an tsaron kasar guda shida.


Tun a cikin watan Yunin shekara ta 2012 ne wata kotu a kasar Masar ta zartar da hukuncin daurin rai da rai a gidan kurkuku kan tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak, sannan a cikin wannan wata na Ogusta babbar kotun daukaka kara a kasar ta Masar ta bada umurnin sakinsa tare da sake gudanar da wata sabuwar shari'a kan zarge-zargen da ake yi kansa.



1277995



captcha