Kamfanin ilalncin labaran iqna ya habarta cewa, baya ga kisann mabiya addinin muslunci yan ta;addan kasar Syria da ke samun goyon bayan kasashen yammacin turai sun wulaknta kur’ani mai tsarki a wasu wurare da suka kai hare-hare a cikin lokutan nan a kasar.
A wani labarin kuma na daban, shugaban Haramtacciyar Kasar Isra’ila Shemon Perez ya ce; Abinda ya ke faruwa a Syria ladabtar da ita ce saboda ta ki yin sulhu da su. A yau lahadi ne Shemon Perez ya gabatar da jawabi a wurin bikin tunawa da yakin 1973 wanda kasashen Masar da Syria su ka yi da ‘yan yan sahayoniya ‘yan mamaya, ya fada a fili cewa; Kin amincewar da Hafizul-Asad ya yi da sulhun da Anwar Sadat ya kulla, shi ne dalilin rusa kasar Syria da ake yi a yanzu.
Perez ya ci gaba da cewa; A wannan lokacin al’ummar Syria suna dandana kudarsu ne saboda kin amincewar Asad da sulhu. Yakin shekarar 1973 wanda a kasashen Syria da Masar ake kiransa da “yakin Watan Oktoba” ya afku ne a tsakanin kasashen larabawan biyu da kuma h.k. Isra’ila, wanda ya yi sanadiyyar halaka sojojin yahudawa 2569, da kuma kame wasu 301. Shugaban kasar Masar na wancan lokacin Anwar Sadat ya rattaba yarjejeniyar sulhu da h.k. Isra’ila, yayin da kasar Syria ta ki amincewa da shi.
Furucin na Shemon Perez ya zo ne a matsayin tabbatar da abinda gwamnatin Syria da kuma kasashen da dama su ke fada na cewa, abinda ya ke faruwa a wannan kasa ba shi da alaka da yunkurin samar da sauyi a fagen siyasa, makirci ne da makarkashiya da manyan kasashe da su ka hada da h.k. Isra’ila su ka kitsa.
1288612