کد خبر: 1280024
تاریخ انتشار : ۰۷ شهريور ۱۳۹۲ - ۱۳:۴۹

Sakataren Tsaron Amurka Ya Yi Da'awar Cewa Zasu Kaddamar Da Hari Kan Kasar Siriya

Bangaren kasa da kasa, Sakataren tsaron kasar Amurka ya yi furuci da cewar gwamnatin Amurka ba zata dauki wani matakin soji kan kasar Siriya ba har sai ta samu goyon bayan duniya kuma karkashin doka.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A bayanin da ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta fitar yana dauke da cewar sakataren tsaron kasar ta Amurka Chuck Hagel ya bayyana cewar Amurka tana cikin shirin mai da martani kan amfani da makamai masu guba a kasar Siriya amma duk wani matakin da zasu dauka sai ya kasance da goyon bayan duniya kuma a kan doka.


Ita kuwa kasar Turkiyya ta bayyana cewar tana cikin shirin taimakawa a harin da za a kaddamar kan kasar Siriya koda kuwa babu amincewar Majalisar Dinkin Duniya, a gefe guda kuma kasashen Iran, Rasha da Iraki sun yi gargadi kan duk wani gigin daukan matakin soji kan kasar Siriya.


Kamar yadda gwamnatin Jamhuriyar Niger ta fitar da sanarwar cewa kamata ya yi kafin daukan duk wani matakin soji kan kasar Siriya a jira sakamakon binciken tawagar masu binciken Majalisar Dinkin Duniya. Wannan shi ne karon farko da aka samu wata kasa a yammacin Afrika da ta fito fili ta bayyana matsayinta kan yakin da Amurka da kawayenta ke kokarin kadamarwa kan kasar Siriya.


1279754



captcha