iqna

IQNA

Bangaren siyasa, Ayatollah Imam Kashani limamin da ya jagoranci sallar juma'a a nan birnin Tehran ya bayyana cewa jamhoriyar musulinci na cikin yaki da rudun tattalin arziki na makiya kuma cikin yardar Allah za ta fita daga wannan matsala.
Lambar Labari: 3482880    Ranar Watsawa : 2018/08/10

Bangaren kasa da kasa, a yau ne aka gudanar da aikin kakkabe kura a kan kabarin Imam Ridha (AS) da kuma tsaftace habbarensa mai tsarki da ke Mashhad.
Lambar Labari: 3482879    Ranar Watsawa : 2018/08/10

Bangaren kasa da kasa, wani harin sama da kawancen da Saudiyya ke jagoranta a yakin Yemen, ya yi sanadimin mutuwar yara 'yan makaranta a kalla 39 tare da jikkata wasu mutane 48 na daban a arewacin kasar ta Yemen.
Lambar Labari: 3482877    Ranar Watsawa : 2018/08/09

Bangaren kasa da kasa, an tarjama littafin rayuwar jagoran juyin juya halin muslunci na Iran a kasar Iraki.
Lambar Labari: 3482876    Ranar Watsawa : 2018/08/09

Bangaren kasa da kasa, an ware kyautar wasu kudade da za a bayar ga yara wadanda suke yin sallar asuba a masallaci a lardin Buhaira na Masar.
Lambar Labari: 3482875    Ranar Watsawa : 2018/08/09

Bangaren kasa da kasa, karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Senegal ya dauki nauyin shirya wani horo na koyar da fasahar kayata rubutun kur’ani.
Lambar Labari: 3482874    Ranar Watsawa : 2018/08/08

Bangaren kasa da kasa, domin tabbatar da tsaro ga tawagar maniyyata daga kasar Ghana gwamnatin kasar ta dauki matakai na musamman.
Lambar Labari: 3482873    Ranar Watsawa : 2018/08/08

Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar nazarin addinin musulunci ta Iman da ke kasar Austria za ta gudanar da wani shiri na bayar da horo kan ilmomin musulunci.
Lambar Labari: 3482872    Ranar Watsawa : 2018/08/07

Bangaren kasa da kasa, wata cibiyar musulmi a gabashin Saudiyya ta sanar da shirinta na taimaka ma maniyyata da wani tsari na sahihin karatun gajerun surorin kur’ani.
Lambar Labari: 3482871    Ranar Watsawa : 2018/08/07

Bangaren siyasa, A wata zantawa da da ya yi a daren jiya da tashar talabijin ta daya ta kasar Iran, shugaban kasar ta Iran Hassan Rauhani ya bayyana takunkumin da Trump ya kakaba wa kasar da cewa, ba zai iya karya lagon Iran ko durkusar da tattalin arzikinta ba.
Lambar Labari: 3482870    Ranar Watsawa : 2018/08/07

Bangaren kasa da kasa, Jiragen saman yakin masarautar Saudiyya sun kai wasu jerin hare-haren wuce gona da iri kan lardunan Sa'adah da Hudaidah da suke kasar Yamen.
Lambar Labari: 3482869    Ranar Watsawa : 2018/08/06

Bangaren kasa da kasa, a hajjin bana za a raba robobin ruwan zamzam guda miliyan bakawai da dubu dari biyar ga alhazai.
Lambar Labari: 3482868    Ranar Watsawa : 2018/08/06

Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar China ta saka wata alama kan katunan ‘alhazan kasar da za su sauke farali a bana.
Lambar Labari: 3482867    Ranar Watsawa : 2018/08/06

Bangaren kasa da kasa, Sheikh Muhammad Bin Rashid Al Maktum sarkin Dubai a wani lamari mai ban mamaki da ba a taba ganin irinsa ba, ya caccaki mahukuntan kasashen larabawa.
Lambar Labari: 3482866    Ranar Watsawa : 2018/08/05

Bangaren kasa da kasa, majalisar musulmin kasar Kenya ta nuna matukar damuwa dangane da karuwar ayyukan cin hanci da rashawa a kasar.
Lambar Labari: 3482865    Ranar Watsawa : 2018/08/05

Bangaren kasa da kasa, an fara aiwatar da wani shiri na koyar da hardar kur’ani mai taken Imamain a garin Samirra na Iraki.
Lambar Labari: 3482864    Ranar Watsawa : 2018/08/05

Bangaren kasa da kasa, Jami'an tsaron kasar Tunisia sun gano gungun wasu mutane masu safarar 'yan ta'adda daga kasar zuwa nahiyar turai.
Lambar Labari: 3482862    Ranar Watsawa : 2018/08/04

Bangaren kasa da kasa, A yau jiragen yakin Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a kan wasu yankuna na zirin Gaza.
Lambar Labari: 3482861    Ranar Watsawa : 2018/08/04

Bangaren kasa da kasa, Mahukuntan kasar Mauritania sun sanar da cewa, ana shirin sake bude mashigar Tanduf da ke kan iyaka tsakanin kasar da kuma Aljeriya nan ba da jimawa ba.
Lambar Labari: 3482860    Ranar Watsawa : 2018/08/04

Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Aljeriya ta bayar da umarnin dakatar da yin amfani da wani kwafin kur'ani mai tsarki a kasar.
Lambar Labari: 3482859    Ranar Watsawa : 2018/08/03