iqna

IQNA

Bangaren kasa da kasa, a gasar kur’ani karatun kur’ani mai tsarki ta duniya ta mata zalla wadda ta wakilci Iran ta zo a matsayi na uku.
Lambar Labari: 3480947    Ranar Watsawa : 2016/11/17

Bangaren kasa da kasa, Al'ummar yankin Lisasafah da ke cikin gundumar kazablanka a kasar Morocco sun gudanar da wani gangami a yau domin nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a yankin.
Lambar Labari: 3480946    Ranar Watsawa : 2016/11/16

Bangaren kasa da kasa, kungiyoyin kare hakkin bil adama sun ce har yanzun jami'an tsaron kasar Myanmar suna ci gaba take hakkin musulman Rohinga na kasar.
Lambar Labari: 3480945    Ranar Watsawa : 2016/11/16

Bangaren kasa da kasa, hukumomi a Iraki sun ce ya zuwa yanzu 'yan kasashen waje kimanin miliyan daya da rabi ne suka shiga cikin Iraki domin ziyarar arba'in na Imam Hussain (AS) a Karbala.
Lambar Labari: 3480944    Ranar Watsawa : 2016/11/16

Bangaren kasa da kasa, wata kotu a kasar Sudan ta yanke hukuncin daurin shekara guda a gidan kaso da bulala 40 a kan wani barawon kur’ani mai tsarki.
Lambar Labari: 3480943    Ranar Watsawa : 2016/11/15

Bangaren kasa da kasa, a jiya ne aka ga wata mafi girma kasashen duniya daban-daban da hakan ya hada har da hubbaren Abul Fadhl Abbas (AS) a Karbala.
Lambar Labari: 3480942    Ranar Watsawa : 2016/11/15

Bangaren kasa da kasa, Hussain Mirzaei Vani jakadan Iran a kasar Venezuela ya bayyana a zantawarsa da radio ALBA CIUDAD cewa wasikar jagora zuwa matasan turai ta yi tasiri.
Lambar Labari: 3480941    Ranar Watsawa : 2016/11/15

Wata Sabuwar Muslunta A Amurka:
Bangaren kasa da kasa, wata mata ba'amurka mai suna Liza Shanklin ta sanar da karbar addinin muslunci sakamakon yin bincike a cikin kur'ani mai tsarki.
Lambar Labari: 3480940    Ranar Watsawa : 2016/11/14

Bangaren kasa da kasa, cibiyar muslunci ta Hamburg za ta gudanar da tarukan makokin goman karshen watan safar.
Lambar Labari: 3480939    Ranar Watsawa : 2016/11/14

Bangaren kasa da kasa, an kafa wasu tantuna na karatun kur'ani a inda ake yada zango ga masu tattakin arbain na Imam Hussain (AS) daga Najaf zuwa Karbala.
Lambar Labari: 3480938    Ranar Watsawa : 2016/11/14

Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da zaman taron kawara juna sani kan ma’anar kyamar musulunci wanda zai gudana a birnin Alkahira na kasar Masar.
Lambar Labari: 3480937    Ranar Watsawa : 2016/11/13

Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar Republican sun ziyarci wani masallaci na musulmi a garin Starling da ke cikin jahar Virginia.
Lambar Labari: 3480936    Ranar Watsawa : 2016/11/13

Bangaren kasa da kasa, Zakaran dambe na kasar Birtaniya Tyson Fury ya sanar da karbar addinin muslunci, inda ya mayar da sunansa Riaz Tyson Muhammad, kamar yadda ya sanar a shafinsa na twitter.
Lambar Labari: 3480935    Ranar Watsawa : 2016/11/13

Bangaren kasa da kasa, wasu daga daliban jami'a musulmi a birnin New York sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da kyamar musulmi.
Lambar Labari: 3480933    Ranar Watsawa : 2016/11/12

Bangaren kasa da kasa, an fara gudana r da wani zaman taro na karawa juna sani kan addinin muslunci a jami'ar Haidelburg da ke kasar Jamus.
Lambar Labari: 3480932    Ranar Watsawa : 2016/11/12

Bangaren kasa da kasa, Sheikh Muhammad Mahmud Tablawi shugaban kungiyar makaranta kur'ani ta kasar Masar y ace yana kyau iyaye su koyar da yaransu karatu tun suna kanana.
Lambar Labari: 3480931    Ranar Watsawa : 2016/11/12

Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramta wa dubban mutane daga Gaza halartar sallar juma’a a birnin Quds.
Lambar Labari: 3480930    Ranar Watsawa : 2016/11/11

Bangaren kasa da kasa, babban kwamandan rundunar da ke kula da ayyukan tsaro na yankin Furat ya bayyana cewa fiye da jami’an tsro dubu 30 ne za su gudanar da ayyukan tsaro a taron arba’in.
Lambar Labari: 3480929    Ranar Watsawa : 2016/11/11

Bangaren kasa da kasa, an sake saka kalaman da zababben shugaban kasar Amurka yay i a na neman a hana musulmi shiga Amurka da kuma krarsu daga kasar a shafinsa.
Lambar Labari: 3480928    Ranar Watsawa : 2016/11/11

Bangaren kasa da kasa, Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Spain ta sanar da cewa 'yan sandan kasar sun sami nasarar tarwatsa 'yan wata kungiyar 'yan ta'adda da suke kokarin janyo hankula kananan yara da matasa da shigar da su cikin kungiyar ta'addancin nan ta Da'esh (ISIS) a kasar.
Lambar Labari: 3480927    Ranar Watsawa : 2016/11/10