صفحه نخست

فعالیت قرآنی

سیاست و اقتصاد

بین الملل

معارف

اجتماعی

فرهنگی

شعب استانی

چندرسانه ای

عکس

آذربایجان شرقی

آذربایجان غربی

اردبیل

اصفهان

البرز

ایلام

خراسان جنوبی

بوشهر

چهارمحال و بختیاری

خراسان رضوی

خراسان شمالی

سمنان

خوزستان

زنجان

سیستان و بلوچستان

فارس

قزوین

قم

کردستان

کرمان

کرمانشاه

کهگیلویه و بویر احمد

گلستان

گیلان

لرستان

مازندران

مرکزی

هرمزگان

همدان

یزد

بازار

صفحات داخلی

کد خبر: ۱۲۷۸۵۳۸
تاریخ انتشار : ۰۴ شهريور ۱۳۹۲ - ۱۷:۵۷

Bangaren kasa da kasa, Lauyan da ke kare shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood a kasar Masar ya zargi jami'an tsaron kasar da cin zarafin wanda yake wakilta Muhammad Badi'i a wajen da suke tsare da shi.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, Muhammad Gharib lauyan shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi ta kasar Masar ya bayyana cewar jami'an tsaron Masar sun dauki matakin cin zarafin Muhammad Badi'i dan shekaru 70 a duniya a wajen da suke tsare da shi ta hanyar duka, zagi da furta munanan maganganu ga mahaifansa.


Lauya Muhammad Gharib ya kara da cewar sakamakon naushin da jami'an tsaron Masar suka yi wa Muhammad Badi'i a fuska ya janyo faduwar hakorarsa na ruba, kuma farmakin da suka kai gidanasa ya janyo lalata gidan.


Tun a cikin makon da ya gabata ne dai jami'an tsaron Masar suka kame shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi ta kasar Muhammad Badi'i da mataimakinsa Khairat Al-Shater da Rashad Bayoumy kan zargin kunna wutar tarzoma da rikici a kasar Masar da ta lashe rayukan daruruwan mutane tare da jikkatan wasu dubbai na daban bayan kifar da gwamnatin Muhammad Morsi.



1278403