صفحه نخست

فعالیت قرآنی

سیاست و اقتصاد

بین الملل

معارف

اجتماعی

فرهنگی

شعب استانی

چندرسانه ای

عکس

آذربایجان شرقی

آذربایجان غربی

اردبیل

اصفهان

البرز

ایلام

خراسان جنوبی

بوشهر

چهارمحال و بختیاری

خراسان رضوی

خراسان شمالی

سمنان

خوزستان

زنجان

سیستان و بلوچستان

فارس

قزوین

قم

کردستان

کرمان

کرمانشاه

کهگیلویه و بویر احمد

گلستان

گیلان

لرستان

مازندران

مرکزی

هرمزگان

همدان

یزد

بازار

صفحات داخلی

کد خبر: ۱۲۸۲۳۴۶
تاریخ انتشار : ۱۲ شهريور ۱۳۹۲ - ۱۷:۵۷

Bnagaren kasa da kasa, tawagar ‘yan majlaisar dokokin kasar Syria da ta kai ziyara a kasar Lebanon ta gana da babban sakataren kungiyar hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah dangane da abubuwan da suke faruwa aSyria da kuma yunkurin kasashen turai an kai wa kasar harin soji.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya ce a wani labarin kuma kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta bukaci duniya ta dauki matakin hukunta gwamnatin Siriya kan zargin amfani da makamai masu guba a kasarta.



A karshen zaman gaggawa da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa suka gudanar a yammcin jiya Lahadi a birnin Alkahira na kasar Masar sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da dukkanin kungiyoyin kasa da kasa da gwamnatocin kasashe kan su yi aiki da hakkin da ya rataya a kansu kamar yadda dokokin kasa da kasa suka shimfida kan mummunar laifin da aka tafka na amfani da makamai masu guba a kasar Siriya.


Bayanin bayan taron ministocin harkokin wajen kasashen da suke mambobi ne a kungiyar hadin kan Larabawa karkashin matsin lambar kasar Saudiyya ya daura alhakin laifin amfani da makamai masu guba a Siriya kan gwamnatin kasar tare da yin kira ga gurfanar da dukkanin wadanda suke da hannu a amfani da muggan makamai masu guba a gaban kotun kasa da kasa domin hukunta su, duk kuwa da cewar kasashen Masar, Iraki, Labanon, Tunusiya da Aljeriya sun fito karara sun jaddada rashin amincewarsu da duk wani shirin daukan matakin soji kan kasar ta Siriya.


Zaman ministocin harkokin wajen kasashen Larabawan ya daura alhakin amfani da makamai masu guba kan gwamnatin kasar Siriya ne ba tare da gabatar da wani dalili da ke tabbatar da hannunta a amfani da makaman ba ko jirar sakamakon binciken tawagar masu binciken Majalisar Dinkin Duniya lamarin da ke kara janyo sanya alamar tambaya kan matsayin kungiyar ta kasashen Larabawa da uwayen gijinsu na yammacin Turai kan kasar Siriya.


1282219